KYAUTATA ZUKATA
This ebook may not meet accessibility standards and may not be fully compatible with assistive technologies.
A wannan littafin mai ban sha'awa, mai ratsa zuciya da tsokano tunani, marubucin (Salisu Mika'ilu) ya kawo mana hanyoyin da za mu bi wajen ganin mun ginawa kanmu kyawawan dabi'u da halaye, ya kuma nusar da mu amfani da fa'idojin neman ilimi da kuma muhimmancin dogaro da Kai.
Ta hanyar amfani da misalai masu kyau da labarai masu hikima da kama zuciya, wannan littafin yana nunawa masu karatu, ba tare da banbanci a shekaru ko matsayin su ba, yadda za su gina tunani, dabi'u da halayen da suka zama dole mutum ya mallaka matukar yana son yayi nasara a rayuwarsa. Ba wani banbanci, so kake ka inganta rayuwar ka, ko so kake ka k'arfafi wani, ko dai kawai kana so ne kayi rayuwa mai cikakkiyar manufa, wannan littafin dukiya ce mai darajar da ba ta misaltuwa.
Don haka, kayi himma wajen shiga wannan taska mai sauya rayuwa don gano karfi da tasirin kyautata dabi'u, muhimmancin neman ilmi da kuma dogara da kai.
Details
- Publication Date
- Feb 12, 2025
- Language
- Hausan
- Category
- Education & Language
- Copyright
- All Rights Reserved - Standard Copyright License
- Contributors
- By (author): Salisu Mikailu Birnin Kudu
Specifications
- Format